Sani Dan IndoNigeria |1951| HausaFitaccen mawakin nan na kasar Hausa a Najeriya, Alhaji Sani Dan-Indo, ya rasu.Wasu makusantan mawakin sun shaida wa BBC cewa Sani Dan-Indo, ya rasu ne a birnin Kano.Mawakin, wanda ya rasu yana da shekara 55 a duniya, ya bar mata daya da 'ya'ya shida.Zubairu, da ya daga cikin 'ya'yan margayin ya ce sun rabu lafiya da daddare a ranar Lahadi, amma kuma da asuba a ranar Litinin, Allah ya dauki ransa. Marigayi Sani Dan Indo ya yi wakoki da dama a fannoni daban-daban da suka hada da noma da al'ada da kuma zamantakewa wadanda suka yi fice a kasar Hausa.Daga cikin wakokinsa akwai "Dan-Indo Mutumin Gaskiya", wacce ta shahara sosai.
A shekarar 2011 ya samu sabani da hukumar tace fina-finai ta jihar Kano, saboda ya yi wasu wakoki da hukumar ta ce ba su dace ba, kuma hakan ya sa aka yanke masa hukuncin daurin wata shida a gidan kurkuku.